✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a mayar da waɗanda Lakurawa suka raba da garuruwansu – Gwamnan Kebbi

Nasir Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin ƴangudun hijira

Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya tabbatarwa mutanen da hare-haren Lakurawa a ƙaramar hukumar Arewa ya raba da muhallansu cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan gaggawa domin mayar da su garuruwansu.

Nasir Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin ƴangudun hijira da ke Kangiwa a jihar ranar Laraba.

Sansanin ya tanadi waɗanda suka rasa muhallansu daga garuruwan Birnin Debe da Dan Marke, da Tambo, ne ke samun mafaka a sansanin inda wasu mahara ɗauke da makamai suka kai hari a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda suka kashe mutum 11 tare da ƙona gida ɗaya daga cikin ƙauyukan.

A wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Yahaya Sarki ya fitar, ta ce Gwamna Idris ya kai ziyarar ne domin jajanta wa mutanen tare da ganewa idonsa halin da suke ciki, domin sanin matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka.

Idris wanda ya bayyana alhininsa kan asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi, ya yaba wa jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suke yi na shawo kan rikicin.

Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake yawan samun hare-haren daga Jihar Sakkwato da ke maƙwabtaka da Jamhuriyar Nijar.

“Na yaba wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Arewa bisa gaggauta kafa sansanin ‘yan gudun hijira kamar yadda na umarce shi.