✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kirkiro sabuwar rundunar yaki da miyagun ayyuka – Sufeto Janar 

  Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Alhaji Muhammed Adamu, ya ce za a kirkiro sabuwar rundunar ’yan sandan da za ta yi aikin dakile…

 

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Alhaji Muhammed Adamu, ya ce za a kirkiro sabuwar rundunar ’yan sandan da za ta yi aikin dakile miyagun ayyuka da suka addabi al’umma.

Sufeto Janar din ya ce, gudunmawar kowa a fannin bayar da labarin bullar miyagu ga mahukunta zai taimaka wajen samun nasarar sabuwar rundunar.

Sufeto Janar din ya fadi haka ne a wajen taron tsaro da aka yi a Ibadan ranar Litinin da ta gabata inda gwamnoni 6 da manyan sarakuna da shugabannin kungiyoyi jama’a da na addinai da dukkan masu ruwa-da- tsaki a Kudu maso Yamma suka halarta.

Ya ce an kama mutum 552 da ake zargi da kisan kai a fadin kasar nan a tsakanin watan Janairu zuwa Agusta bana, inda mutum 66 suka fito daga Kudu maso Yamma. “Haka jimillar mutum 2,015 da ake zargi da fashi da makami aka kama, kuma an samu 363 daga wannan sashi yayin da aka kama mutum 1,154 kan zargin satar mutane, kuma wannan sashi ya samar da mutum 147 daga cikinsu,” inji shi.

Ya ce kirkiro da shirin ‘Operation Puff Adder’ da Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta yi ya taimaka sosai wajen rage aukuwar miyagun ayyuka a kasar nan. Sai dai ya nuna muhimmancin ganin kowa yana bayar da gudunmawarsa ta fannin bayar da rahoton bullar miyagun ayyuka a wurin da yake zaune.

Gwamnonin da sauran masu ruwa-da-tsakika Kudu maso Yamma, sun bayar da shawarawari ta hanyar da suke ganin za a yi amfani da ita wajen magance miyagun ayyuka da suke zama barazana ga tsaron kasa.

Da yake karanta sakamakon bayan taron a madadin gwamnonin da Sufeto Janar a babban zauren taro na Jami’ar Ibadan, mai masaukin baki Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, ya ce sun amince da fara yin aiki da na’urar zamani CCTB da ke daukar hoto da bidiyo a kan hanyoyi da wuraren taron jama’a. Kuma sun amince da kirkiro da dakarun lalubo rahoton sirri  da za a samar da su  a unguwanninsu don taimakawa wajen rage aukuwar miyagun ayyuka a cikin jama’a.

Gwamna Makinde, ya ce mutanen da suka hada da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da kungiyoyin OPC da ta direbobi ta  NURTW da Miyetti Allah ne za su samar da mutanen da za su yi wannan aiki a wuraren da suke zaune.

Gwamnonin yankin sun yi alkawarin bayar da tallafin motoci da kayan aiki ga sabuwar rundunar yaki da miyagun ayyuka da Sufeto Janar ya kirkiro domin zamanantar da tsaro a Najeriya.

Sarkin Legas Oba Rilwanu Akiola ya fadi a wurin taron cewa “Karancin kudin da ake ware wa ’yan sanda ne babban abin da ke kawo matsalar tsaron.” Kuma ya nuna rashin amincewa da samar da ’yan sandan jihohi, inda ya ce, muhimmin abin da kasa take bukata shi ne rahoton bullar miyagun ayyuka daga al’ummomi.

Shi kuwa Alake na Egba, Oba Adedotun Gbadebo kira ya yi ga mahukunta su shawo kan matsalolin talauci da rashin aikin yi a tsakanin matasan kasar nan domin matsalar tsaro a kasa ba sabuwar aba ba ce.

A shawarar Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, cewa ya yi akwai Yarbawa da yawa da ke zaune a kasashen waje da suka kasa dawowa gida saboda tabarbarewar tsaro a Najeriya. Ya yi gargadin cewa, kada a kuskura a tsoma siyasa a cikin matsalar tsaron kasa.

Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji wanda Sanata Lekan Balogun, ya wakilta cewa ya yi sarakunan yankin za su yi duk abin da suke iyawa wajen ganin an cimma wannan buri na kyautata tsaron kasa domin kare lafiya da dukiyar jama’a.