✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a karawa masu yin NYSC kudi da aka tura karkara a Anambra – Gwamna Obiano

Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta karawa masu yi wa Kasa Hidima na NYSC, wadanda aka tura yankunan karkara…

Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta karawa masu yi wa Kasa Hidima na NYSC, wadanda aka tura yankunan karkara kudaden alawus-alawus.

Gwamnan, wanda Kwamishinan Tallafawa Matasa na Jihar kuma Shugaban Hukumar ta NYSC na Jihar, Onarabul Afam Mbanefo ya wakilta ya yi shelar hakan a lokacin bukin kammala zaman sansanin horaswa na jami’an NYSC rukunin B kuma zubin Farko, a sansanin wucin gadin da ke garin Umuanya.

Gwamna Obiano,  ya ce tuni gwamnatin ta yi nisa wajen yadda za ta fara biyan karin kudaden alawus-alawus ga Jami’an yi wa kasa Hidiman da aka tura yankunan karkara.

Ya kuma ce, ya bayar da umurni ga dukkanin ma’aikatun da aka tura wa Jami’an NYSC da ka da su ki karbar su, in ma dai a ma’aikatun Jihar ne ko kuma na Kananan Hukumomi.