Shugaba Buhari ya umarci Hukumar Tsara Albashi ta Kasa da ta fito da sabon tsarin albashi da alawus-alawus na jami’an ’yan sanda a Najeriya.
Buhari ya bayyana hakan ne a bukin yaye kananan hafsoshin ’yan sanda 418 karo na uku da ya gudana a Kwalejin ’Yan Sanda da ke Wudil a Jihar Kano, ta bakin Ministan Ayyukan ’Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi.
Shugaban ya jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da daukar jami’an ’yan sanda 10,000 a kowace shekara da nufin magance matsalar karancin jami’an tsaron da rundunar ke fama da ita.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu an sake farfado da Kwamitin Karbar Koke-koken Jama’a batun cin zarafi da take hakki daga jami’an ’yan sanda.