Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya ba da tabbacin cewa za a kammala aikin titin Kano zuwa Abuja kafin 29 ga watan Mayun 2023.
Ya ba da tabbacin ne ranar Juma’a, lokacin da yake duba aikin titin a kan iyakar Jihohin Kano da Kaduna.
- Haramcin amfani da mutum-mutumi a Kano na nan daram – Hisbah
- ’Yan fashi sun yi wa motar banki luguden wuta
Sai dai Fashola ya ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun yi ingantaccen aikin da za a jima ana amfana da shi.
A cewarsa, “Burinmu shi ne mu tabbatar mun kammala aikin nan kafin ranar 29 ga watan Mayun 2023, amma akwai kalubale iri-iri da muke fama da su.
“Ba za mu sadaukar da burinmu na yin ingantaccen aiki ba saboda sauri, amma muna iya kokarinmu, kuma Shugaban Kasa ma ya damu matuka wajen ganin an kammala wannan aikin.
“Wannan hanya ce mai cike da hada-hadar ababen hawa, saboda akalla motoci 20,000 suna bin ta a kullum, ka ga ba zaka rufe ta ba gaba daya, wadannan sune wasu daga cikin kalubalen da muke fuskanta,” inji shi.
Sai dai Ministan ya ce daga abin da ya gani, ya gamsu da yadda ’yan kwangila ke gudanar da aikin.