✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a kafa dokar hana shan sigari a New Zealand

Dokar na son dakile matasan kasar da fara shan sigari.

Kasar New Zealand na yunkurin kafa wata sabuwar doka da za ta haramta wa matasan kasar shan sigari.

Sabuwar dokar da ake shirin kafawa za ta hana duk wani matashi dan kasa da shekara 18 ta’ammali da sigari, da zummar ganin matasa masu tasowa sun guje ta tun a farkon kuruciyarsu.

Ministar Lafiyar Kasar, Dokta Ayesha Verrall, ta bayyana a ranar Alhamis cewa, “Mun san ganin matasa ba su fara shan sigari ba, saboda haka za mu kafa tsattsauran hukunci ga wadanda suke sayar da ita da kuma masu shan ta.

“Idan aka kafa dokar hakan zai hana matasa ’yan shekara 14 shan sigari a hukumance.”

Gwamnatin kasar na shirin mika kudurin dokar ga majalisar dokokin kasar a 2022, a yunkurinta na rage shan sigari da kashi biyar cikin 100 a shekara a 2025.

Alkaluman gwamnatin kasar sun nuna kashi 13.4 cikin 100 na matasan New Zealand na shan sigari.

Sai dai adadin ya ragu da kashi 18.2 cikin 100 a tsakanin 2011 da 2012.

Mutum 4,000 zuwa 5,000 ne a kasar ke mutuwa a sakamakon ta’ammali da sigari, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana.

“Shan sigari na daga cikin abubuwan da ke haifar da mace-mace da kuma kamuwa da cutar dajia New Zealand,” a cewar Verrall.