✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a iya kawo karshen ’yan ta’adda a Gombe – Sarkin Taurin Tangale

Sarkin Taurin Tangale Alhaji Lauwali Bala’i wanda ya yi fice wajen yakar masu garkuwa da mutane da ’yan fashi a Kudancin Gombe ya bayyana yadda…

Sarkin Taurin Tangale Alhaji Lauwali Bala’i wanda ya yi fice wajen yakar masu garkuwa da mutane da ’yan fashi a Kudancin Gombe ya bayyana yadda rashin tallafi ke kawo masa cikas a aikin da yake yi na sa-kai.

Sarkin Taurin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce suna bukatar tallafi don su ci gaba da shiga daji suna kamo masu garkuwa da mutane da barayin shanu da suka addabi dajin Billiri da ya yi iyaka da dajin Jihar Taraba.

Alhaji Lauwali ya ce duk kokarin da yake yi, shi yake daukar dawainiyar kansa da yaransa suna shiga daji su kwana.

Ya ce Mai martaba Mai Tangale Dokta Abdu Buba Mai Sheru ne kawai yake taimaka masa yake samun saukin aiki da ya sa kansa, sai ya yi kira ga ’yan siyasa da daidaikun mutane da gwamnati su taimaka musu da kayayyakin aiki na shiga daji.

“Idan aka ba mu kayan aiki, a dajin nan ba inda barayin nan za su tsere mana saboda mun san ko’ina a ciki, amma da yake akwai kwarurruka shi ya sa mota ba ta shiga ko’ina, idan muka bi su in suka bi wani wajen da mota ba za ta bi ba, sai su tsere mana amma duk da haka muna kama wadansu domin yanzu haka ina da barayin da muka kama da yawa,” inji shi.

Alhaji Lauwali ya roki dan majalisar jihar mai wakiltar  Billiri Mista Rambi Ibrahim Ayala Gamzakin Tangale, ya taimaka musu da babura kamar yadda yake raba wa ’yan siyasa don su rika shiga daji don kawar da miyagu.

Kuma ya roki Gwamna Inuwa Yahaya ya taimaka musu da kayan aiki, ya ce idan suka samu taimakon za su iya karade Jihar Gombe da aiki ba iya yankin Billiri kadai ba wajen kawo karshen ’yan ta’adda.

Ya jinjina wa yaransa bisa hadin kai da goyon baya da suke ba shi wajen shiga dajin ba tare da nuna gajiyawa ba.