Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) na shirin haramta wa masu kasa da shekara 18 mallakar layin waya da yin rajistar layin waya.
Hukumar na kuma shirin ba da wa’adin kwana 60 ga masu sabbin layukan waya su fara aiki da su kuma su yi musu rajista ko kuma a tsohe; Sannan tsawon wata biyun, za a kayyade iya irin amfanin da za a iya yi da sabbin layukan.
- Hayakin icen girki na kashe mutum 90,000 a Najeriya
- Jami’an tsaron Ghana sun binciki dan Majalisar Najeriya kan zargin ta’addanci
“‘Mai layin waya shi ne duk mutumin da ya haura shekara 18 da haihuwa da yake yin hulda ko harkokin sadarwa ta hanyar saye ko kulla yarjejeniya da kamfanonin sadarwa masu lasisi,” kamar yadda yake kunshe a cikin daftarin sabuwar dokar NCC, dauke da sa hannun Babban Mataimakin Shuganbanta, Farfesa Umar Garba Danbatta.
Wadannan na daga cikin sabbin tsauraran dokokin yi wa mayu layukan waya rajista a Najeriya da NCC ke neman fitowa da su bayan ta yi wa dokar kwaskwarima.
Wakilinmu ya yi kicibus da kwafin daftarin tsare-tsaren a shafin hukumar, wadda har yanzu take ci gaba da karbar ra’ayoyin masu ruwa da tsaki a bangaren sadarwa game da lamarin.
Dokar ta shardanta cewa dole sai mutum ya cika shekara 18 da haihuwa kafin kamfanonin sadarwa su yi masa rajisatar mallakar layin waya, a matsayin mataki na wucin gadi.
Dokar na kuma shirin sanya wata shida a matsayin wa’adin yin rajistar layukan waya.
Sai dai kuma baki daga kasashen waje ba za a wajabta musu yin rajistar layukansu a Najeriya ba, matukar sun yi wa layukan nasu rajista a kasashensu.