✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gwangwaje malamai da kyautar motoci

Gwamnatin za ta karrama malaman ne don ba su kwarin guiwa game da gudunmawarsu ga ilimi a jihar.

Za karamma wasu malamai da kyautar sabbin motoci da wasu kyaututtuka a matsayain lambar yabo da gwamnatin jihar ke shiryawa duk shekara.

Gwamnatin Jihar Legas ta dauki matakin karamma fitattun malaman ne domin karfafa wa malamai masu tasowa gwiwa su rungumi koyarwa a matsayin aiki na musamman.

Kwamishinar Ilimin Jihar, Folasade Adefisayo, ta shaida wa manema labarai cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu zai ba wa malamai da wasu mutum 13 sabbin motoci kyauta, sannan za a ba wasu 10 kyauta ta musamman.

Malamai 13 da za a karrama na daga cikin mutum 3,000 da suka shiga tsarin bikin karramawar, karkashin tsarin farfado da harkar ilimi na 2020 a jihar.

Ta kara da cewa gwarazan da za a karrama sun fito daga makarantun Firamare, karamar Sakandare da kuma manyan makarantun Sakandare na jihar.

Domin tabbatar da adalci tare da tantance wanda suka shigar gasar, gwamnatin jihar ta kafa kwamiti na musamman, don tantance malaman.

Kwamitin karkashin jagorancin kungiyar makarantu masu zaman kansu ta Najeriya, Lai Koiki, take da alhakin tantance dukkan wanda suka shigar bikin gasar a bana.

A cewar, Kwamishinar Ilimin Jihar, ta ce malaman jihar sun cancanci yabo da tukuici, game da irin ci gaban da suke ba wa ilimi a jihar.

Kazalika, ta ce Gwamna Sanwo-Olu ya bayar da kyautar gida mai dakuna uku ga gwarzon malami da kuma shugaban makaranta na shekarar 2019.