✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gudanar da gasar motsa jiki na matasa a Legas

Hukumar wasan motsa jiki ta kasa wato Athletics Federation of Nigeria ta sanya ranar 6 da 7 na wannan watan (Fabarairu) a matsayin ranakun da…

Hukumar wasan motsa jiki ta kasa wato Athletics Federation of Nigeria ta sanya ranar 6 da 7 na wannan watan (Fabarairu) a matsayin ranakun da za gudanar da gasar motsa jiki ta matasa da kananan yara a filin wasa na Teslim Balogun da ke Jihar Legas.

Gasar wacce ake yi mata lakabi da gasar Dokta Olukoya ta hada wasannin motsa jiki iri-iri wadanda suka hada da guje-guje da kwallon kafa da kwallon Kwando da kwallon Tenis da kokawar zamani da sauransu.
Babban manajan na hukumar motsa jiki na kasa, Yusuf Alli ya bayyana cewa gasar wannan shekara za ta zama zakaran-gwajin-dafi ga gasar motsa jiki ta matasan Afirka da kuma gasar motsa jiki ta matasan duniya.
Alli ya kara da cewa tuni hukumar motsa jiki ta kasa ta fara karbar takardun masu sha’awar shiga gasar ba tare da wata matsala ba.
Ya bukaci jihohi da kungiyoyi wadanda suke bukatar shiga gasar su hanzarta shiga tun kafin hukumar ta rufe karbar takardun masu shiga gasar.
Ya ce hukumar ba za ta wuce ranar 2 ga watan Fabarairun na rufe rijistar masu shiga gasar ba.
Hakazalika, za a gudanar da wasannin karshe na gasar makarantun sakandaren Jihar Legas wanda ake yi wa lakabi da Ibile Game 2015 a cikin makon da muke ciki.
Wasu wasanni tuni aka kammala su amma kwallon tenis da fadan Teakwando da kwallon Kwando da wasu wasannin za a ci gaba da gudanar da su a mako mai zuwa.
A wasannin da aka gudanar, makarantar sakandare ta Herbert Macaulay ce ta zama zakara a bangaren kokawar zamani a rukunin kananan yara inda Kwalejin Lagos City College ta yi nasara a rukunin manya.