✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a gina kasuwar hatsi a garin Saminaka

dan Majalisar Dokoki na Jihar Kaduna Mai Wakiltar Mazabar Lere ta Gabas da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, Alhaji Idris Abdullahi, ya bayyana…

dan Majalisar Dokoki na Jihar Kaduna Mai Wakiltar Mazabar Lere ta Gabas da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, Alhaji Idris Abdullahi, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi nisa wajen shirye shiryen gina kasuwar sayar da hatsi a garin Saminaka.
Marafan Saminakan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya.
Ya ce: “A matsayina na mai wakiltar mazabar Lere ta Gabas  a Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, kuma ganin cewa a duk Najeriya babu wurin da ya kai yankin Saminaka noman masara, ya sanya na rubutawa mai girma gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufa’I bukatar a gina mana kasuwar hatsi a garin Saminaka.”
Ya ci gaba cewa tuni gwamnan ya amince a gina musu kasuwar.
Hakazalika, ya ce kwamishinan aikin gona na jihar ya fito ta wani gidan Rediyo, inda ya ce za a yi wannan kasuwar hatsi a garin Saminaka, wadda zata mayar da hankali kan sayar da “masara da waken soya.”
“Babu shakka idan aka gina wannan kasuwa manyan ‘yan kasuwa da kamfanoni za su  rika zuwa har daga kasashen  ketare don sayen kayayyakin amfanin gona,” inji shi.
Bayan haka ya ce ya rubutawa gwamnan game da bukatar  gyara masu   hanyar Saminaka zuwa  Bauchi, wadda ta yi matukar lalacewa, inda ya ce a yanzu an ba da aikin gyara hanyar.
Har’ila yau, ya ce ya yi masa batun hanyar da ta tashi daga Abadawa zuwa Domawa da Sabon fili zuwa Federe da  hanyar Saminaka zuwa unguwar Kura da  hanyar  Kwanar Narbi zuwa Maresu da hanyar  Dokar danbala zuwa Wawan rafi zuwa ’Yarkasuwa.  Kuma ya ce gwamnan ya tabbatar masa da cewa za ayi wadansu daga cikin wadannan ayyukan.
Hakazalika, ya ce  gwamna ya bayar da aikin gyara asibitoci guda 10  a kowace mazaba da ke wannan karamar hukuma, a inda za a gyara asibiti guda daya a kowace mazaba tare da samar da ma’aikata a asibitocin.
Daga nan ya ce, “a halin yanzu ana nan ana  gyara makarantun da suka lalace a yankin tare da samarwa mata da dama aikin dafa abinci a makarantun firamaren yankin.
A karshe ya yi kira ga al’ummar wannan mazaba kan su “kara hakuri su ci gaba da yi mana addu’o’i domin mu samu damar aiwatar da kudurorin raya kasa da muka sanya a gaba,”inji shi.