Gwamnatin Kaduna ta jaddada matsayinta na yin dandaka ga duk namiji ko macen da aka kama ya aikata fyade a jihar.
Kwamishinar Kyautata rayuwa ta jihar, Rabi Salisu ta ce wannan horo ne domin kawo karshe fyade daga kowane jinsi a jihar.
Ta bayyna cewa hukuncin yin dandaka ga maza da mata masu aikata fyade ya yi daidai da dokar jihar na yaki da cin zarafi na 2018.
Kwamishinar ta ce gwamnatin jihar yi dokar ta dandaka ce bayan tuntuban hukumomi da bangarorin da abin ya shafa da kuma wayar da kan al’umma kan illolin fyade.
- Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram Sun Ceto Mata 3
- Safina Namukwaya: Mai shekara 70 ta haifi tagwaye a Uganda
- El-Rufai ya sa hannu kan dokar dandake masu fyade
Ta sanar da hakan ne bayan taron masu ruwa da tsaki da ma’aikatar ta gudanar ranar Alhamis da hadin gwiwar cibiyar inganta lafiya ta bai-daya (CIHP).
Babban jami’in CIHP, Dokta Austin Azihaiwe, ya ce taron na da muhimmanci lalubo hanyoyi da dabarun domin samun nasara wajan yaki da matsalar cin zarafi a cikin al’umma.