✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara yi wa maniyyatan bana bita a Kaduna

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara bita ga maniyyata a dukan sansaninta da ke jihar daga gobe Asabar. Shugaban Hukumar, Imam…

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara bita ga maniyyata a dukan sansaninta da ke jihar daga gobe Asabar.

Shugaban Hukumar, Imam Hussaini Sulaiman Tsoho Ikara ne ya sanar da haka lokacin da yake bayani a cikin wani shirin gidan Radiyon Freedom a Kaduna.

Ya ce hukumar za ta dauki wata hudu tana gudanar da bitar ga maniyatta aikin Hajjin bana.

Ya ce bitar tana da amfani ga maniyyata, don haka su daure su rika zuwa bitar. “Da farko mun so fara bitar ce a mako na biyu cikin watan Fabrairu amma saboda zaben da aka yi sai bai yiwu ba. Amma a yanzu ina farin cikin sanar da maniyatta cewa a ranar Asabar mai zuwa (gobe) za a fara bita ga maniyyatan bana,” inji shi.

Ya ce hukumar za ta taimaka wajen ilimantar da maniyatta a kan yadda kudaden Saudiyya suke da kuma bayani dangane da kudaden kasar Amurka wato Dala.

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna kan yadda take taimaka wa hukumarsa, wanda hakan ke kawo ake samun nasara a lokacin aikin Hajji.