Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin kar ta kwana da zai yi aikin rushe duk wasu gine-gine da aka tsayar ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da haka yayin kaddamar da kwamitin a ranar Litinin.
- Ganduje zai dauki malamai 2000 aiki a Kano
- Muhimman abubuwa kan dan Najeriyar da ya kirkiro rigakafin COVID-19
- Dan sanda ya harbi wani mai kayan lemo a Kebbi
Usman Alhaji ya ce, aikin kwamitin shi ne rushe dukkanin wuraren da aka gina ba bisa ka’ida ba da suka hada da tashoshin mota da masu kasuwanci a gefen titi da wuraren zubar da shara.
Ya bukaci wadanda aka dorawa wannan nauyi da su gudanar da aikin ba sani ba sabo, lamarin da ya ce hakan shi ne kadai matakin da zai taimaka wa kwamitin wajen cin nasara.
Kazalika, ya kuma jaddada cewa gwamnati a shirye take ta bayar da dukkanin goyan-bayan da mambobin kwamitin za su bukata yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Kwamitin zai samu jagorancin Shugaban Hukumar KAROTA na jihar Kano, Baffa Babba Dan Agundi a matsayin shugaba sai Abdullahi Mu’azu shugaban Hukumar Kwashe Shara da Tsaftace muhalli (REMASAB) a matsayin sakataren kwamitin.
A jawabinsa Shugaban Kwamitin Babba Dan Agundi, ya ce za su yi aiki ba sani ba sabo wajen ganin an tsaftace jihar Kano.
Ya kuma bukaci hadin kan jama’ar jihar don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.