✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara rataye masu tukin ganganci a Zamfara

Duk wanda ya yi kisa sai ya biya diyya sannan a yanke masa hukuncin kisa

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta yi dokar hukuncin kisa ga duk direban da aka samu da laifin tukin gangancin da ya yi sanadiyar mutuwa.

Za kuma a tilasta direban biyan diyyar rayukan da ya yi sanadiyar mutuwarsu, baya ga hukuncin kisan da za a yanke masa.

Matawalle ya shaida haka ne a sa’ilin da ya jagorancin tawagar manyan jami’an kamfanin BUA zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, domin yi masa ta’aziyyar rasuwar mutum 15 ’yan masarautar a sakamakon hatsarin mota.

Gwamnan ya yi takaicin mutuwar mutane sakamakon tukin ganganci na diraben babban mota da ya abka wa motar fasinja a kan hanyar Gusau zuwa Funtua.

Ya gwamnatinsa za ta bijiro da tsarin kayyade gudu a kan manyan hanyoyi tare da kayyade nauyin kayan da manyan motoci za su dauka da kuma yi wa direbobi gwajin miyagun kwayoyi a jihar.

“Za mu dauki wadannan matakai ne domin hana tukin ganganci da ke janyo salwatar rayukan jama’a”, inji shi.

Ya sanarwar da ba da naira miliyan biyu ga iyalan kowane magidanci daga cikin mamatan da kuma naira miliyan daya da dubu dari biyar ga iyalan marasa auren daga cikin mamatan.

Ya kara da alkawarin bai wa iyalan kowane mamacin da ya rasu a hatsarin Naira dubu 50 a duk wata har zuwa karshen wa’adin gwamnatinsa.

%d bloggers like this: