Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Anambra, CP Echeng Echeng ya bayar da umarnin kwace duk wani abin hawa da ba shi da sabuwar lambar Najeriyaa Jihar.
Umarnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai Kakakin ’yan sandan a Jihar Misis Nwode Nkiruka ta fitar, a daidai lokacin da ake dab da zaben Gwamnan Jihar a ranar shida ga watan Nuwamban 2021.
- Shugaban Turkiyya, Erdogan, ya fara ziyarar kwana 2 a Najeriya
- Mahaifiyar Shekau: Ni da shi shari’a sai a Lahira
A cewar Kwamishinan, sanarwar ta zo ne bayan umurnin da Babban Sufeton ’Yan Sandan ya bayar na hana ababen hawa marasa lamba da kuma masu bakin gilashi izinin yawo.
Sanarwar ta kuma ce ya zama tilas ’yan sanda su sa ido tare da duba duk wani abin hawa su tabbatar yana dauke da lambar Najeriya.
Bugu da kari, Kwamishinan ya hori jami’an rundunar su sanya ido tare da tabbatar da tsaro musamman a lokacin da ake shirin gudanar da zabe a Jihar.
Ya kuma shawarci bakin da ke shiga Jihar su tabbatar da su ma sun bi dokar sau da kafa.
Sai dai ana ganin sanarwar na zuwa ne bayan mutane a Jihar sun fara amfani da lambobin da ’yan Kungiyar Tabbatar da Kafa Kasar Biyafara (MASSOB) ke sayarwa a matsayin lambobin ababen hawansu. See
Daga karshe ya ce rundanar ta dukufa wajen samar da tsaro ga al’ummar Jihar kafin zabe da kuma bayan zabe.