✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara kama masu karnukan da ba su yi musu rigakafi ba a Anambra

Gwamnatin ta ce karnukan za su iya yada cutar Haukan Kare

Gwamnatin jihar Anambra ta bukaci masu karnukan da ba a yi musu rigakafin cutar haukan kare ba da su daina barinsu suna gararamba a kan tituna ko a fara kama su.

Gwamnatin ta ce muddin irin wadannan karnukan suka ciji wani mutum za a kama mai su kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Kwamishinan Aikin Gona na jihar, Dokta Forster Ihejiofor, ne ya yi gargadin yayin bikin kaddamar yi wa karnukan rigakafin na shekarar 2022 a Awka, babban birnin jihar.

An dai shirya bikin ne saboda Ranar Cutar Haukan Kare ta Duniya ta bana a jihar.

A cewar Kwamishinan, yin rigakafin ga karnukan, wadanda su ne manyan masu yada cutar, ita ce babbar hanyar kawar da cutar. (NAN)