Gwamnatin jihar Anambra ta bukaci masu karnukan da ba a yi musu rigakafin cutar haukan kare ba da su daina barinsu suna gararamba a kan tituna ko a fara kama su.
Gwamnatin ta ce muddin irin wadannan karnukan suka ciji wani mutum za a kama mai su kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.
- Sojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 4, sun jikkata sama da 40
- ASUU: Sam gwamnatin Buhari ba ta muntunta Ilimi – Sanusi
Kwamishinan Aikin Gona na jihar, Dokta Forster Ihejiofor, ne ya yi gargadin yayin bikin kaddamar yi wa karnukan rigakafin na shekarar 2022 a Awka, babban birnin jihar.
An dai shirya bikin ne saboda Ranar Cutar Haukan Kare ta Duniya ta bana a jihar.
A cewar Kwamishinan, yin rigakafin ga karnukan, wadanda su ne manyan masu yada cutar, ita ce babbar hanyar kawar da cutar. (NAN)