✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara daure ’yan kungiyar asiri shekaru 21 a Legas

An kirkiro dokar ne dai domin a haramta ayyukan kugiyoyin matsafa a jihar da ma sauran masu alaka da su

Majalisar Dokokin Jihar Legas ta zartar da wani kuduri zuwa doka da zai kawo karshen ayyukan ’yan kungiyoyin asiri a jihar.

Sabuwar dokar dai ta tanadi hukuncin daurin shekaru 21 ga dukkan wanda aka samu yana aikata ayyukan kungiyar asiri, sai kuma daurin shekaru 15 ga dukkan wanda ya basu matsuguni a matsayin wurin taruwarsu.

An kirkiro dokar ne dai domin a haramta ayyukan kugiyoyin matsafa a jihar da ma sauran masu alaka da su don a tabbatar da kare lafiya da walwalar jama’a.

Kazalika, hukuncin zai kuma shafi duk wanda aka kama ya halacci tarukan irin wadannan kungiyoyin inda za a yi musu kudin goro wajen hukuntawa.

Dokar ta kuma ce duk wanda aka samu da hannu wajen tilastawa mutane su shiga kungiyar asiri a jihar ya cancanci hukuncin daurin shekaru 15, yayin da kuma wanda ya kai hari ko ya ji wa wani rauni da sunan tilasta masa shiga kungiyar ya aikata laifin da za a iya daure shi shekaru 21.

Har ila yau, dokar ta shafi hatta dalibai dake makarantun jihar, inda su ma za a iya daure duk wanda aka tabbatar ya aikata laifin a gidan yari shekarun da ba su haura biyu ba.

Bayan amincewa da dokar ne, Kakakin Majalisar, Mudashiru Obasa ya umarci Akawun Majalisar, Olalekan Onafeko da ya mika ta zuwa ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu domin ya rattaba mata hannu.

%d bloggers like this: