Sojojin da ke mulkin Myanmar a ranar Talata sun yi barazanar daurin shekara 10 a kurkuku ga duk wanda suka samu ya yi ‘liking’ ko ‘sharing’ abubuwan ’yan adawar kasar a kafafen sada zumunta.
Kasar dai ta fada cikin rikici tun lokacin da sojojin suka kwace mulkin kasar a 2021, inda wasu kungiyoyi suka dauki makami suna fito-na-fito da sojojin, wasu kuma na neman a dawo da tsarin Dimokuradiyya.
Ministan Yada Labarai na kasar kuma kakakin gwamnatin kasar, Zaw Min Tin, ya ce wasu da suka kira da ’yan ta’adda na neman kudaden da za su wargaza kasar, kuma za su dauki tsattsauran mataki a kan masu goyon bayansu.
Zaw ya ce ba za su lamunci goyon bayan masu fafutukar a kafafen sada zumuntar da masu dauke da makamai ba, kuma duk wanda suka samu yana tallafa musu da kudi, komai kankantarsu zai dandana kudarsa.
Sojojin sun ce sun dauki matakin ne domin su kare kasarsu.
Tun bayan juyin mulkin dai, masu adawa da mulkin sojojin sun rika amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen yada sakonni a ayyukansu da ma yadda sojojin ke cin zarafinsu.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta zargi gwamnatin sojojin da kisan mutane da kuma aikata laifukan take hakkin dan Adam tun bayan juyin mulkin na bara.
An dai kama mutane da dama sannan aka daure wasu masu yawa a shari’ar da aka yi musu a boye.
Ko a kwanan nan sai da aka zartar wa wasu masu fafutukar dawo da mulkin Dimokuradiyya hukuncin kisa, bayan ta zarge su da mara wa kungiyoyi masu dauke da makamai baya. (NAN)