✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara daure ma’aikatan lafiya da na lantarkin da suka shiga yajin aiki shekara 5 a Sri Lanka

Dokar na zuwa ne a daidai lokacin da yajin aikin ma’aikatan lafiyar kasar ya shiga kwana na shida.

Gwamnatin kasar Sri Lanka ta haramta wa ilahirin ma’aikatan lafiya da na lantarki da ke kasar shiga yajin aiki dungurungum.

Kazalika, an tanadi hukuncin daurin shekara biyar a gidan yarin ga dukkan ma’aikacin da ya yi watsi da dokar.

Umarnin, wanda Shugaban Kasa, Gotabaya Rajapaksa, ya bayar ranar Asabar, na zuwa ne a daidai lokacin da yajin aikin da ma’aikatan lafiyar kasar ke yi ya shiga kwana na shida, kuma ya tasamma kassara asibitocin gwamnati a kasar.

Sri Lanka dai ta farfado da tsohuwar dokar da ta kafa ne a shekarar 1979, wacce ta haramta wa ma’aikatan bangarorin biyu duk wani yunkurin tsunduma yajin aiki saboda muhimmancinsu ga al’umma.

Dokar za kuma ba kotuna damar yanke hukuncin daurin shekara biyar tare da damar kwace kadarar duk wanda ya karya ta.

Ko a ranar  Alhamis din da ta gabata dai sai da ma’aikatan suka yi kunnen uwar shegu da umarnin wata kotu da ta umarce su da su janye yakin aikin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da aka shigar a kansu.

Sai dai duk da umarnin, kungiyoyin kwadago na ma’aikatan sun ki janye yajin aikin, inda suka ce suna kan tattauna da lauyoyinsu a kan lamarin

Ma’aikatan Sri Lanka dai na neman karin albashi da kudaden alawus-alawus ne, a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki.

Dubban ma’aikatan ne dai suka shiga yajin aikin, lamarin da ya sa bangaren ba da agajin gaggawa na asibitocin gwamnati ne kawai ke aiki a kasar.

A nasu bangaren kuwa, ko da yake ma’aikatan lafiya ba sa cikin yajin aikin, amma sun yi barazanar bin sahun takwarorin nasu matukar gwamnatin kasar ba ta janye yunkurinta na sayar da wutar lantarkinta ga wani kamfanin kasar Amurka ba.