✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fara amfani da na’urar tantance shigar kwallo a raga a Afirka

Hukumar kula da kwallon kafa a Afirka (CAF) ta ce za ta fara amfani da na’urar zamani wajen tantance ko kwallo ta shiga raga ko…

Hukumar kula da kwallon kafa a Afirka (CAF) ta ce za ta fara amfani da na’urar zamani wajen tantance ko kwallo ta shiga raga ko a’a wato (bideo Assistan Referess, (AbR).

Hukumar ta dauki wannan mataki ne a wata sanarwa da ta fitar a shafin sadarwarta na Twitter a ranar Talatar da ta wuce jim kadan bayan an kammala taron akalan wasanni da ke karkashin hukumar a Cairo da ke Masar.

Ta ce bayan an kammala taron alkalan wasanni ne a hedkwatar hukumar da ke Masar a ranar Litinin da ta wuce, hukumar ta zartar da wannan hukunci.

Na’uar dai ana dasa ta ne a bayan kowace raga a filin kwallon kafa inda da zarar kwallo ta wuce layi za ta sanar da alkalin wasa don ya bayar da ci, haka kuma idan ba ta wuce ba, za ta sanar da shi  don kada ya yi kuskuren bayar da ci.

Sai dai Hukumar CAF ta ce za a fara amfani da na’urar ce a Gasar Cin Kofin Afirka na ’yan gida wato (CHAN) wanda zai gudana a Maroko a tsakanin ranakun 13 ga Janairu zuwa 4 ga watan Fabrairun 2018 a kasar Maroko.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya ta taba amfani da irin wannan na’ura a gasar cin kofin Club World Cup da ya gudana a Japan da kuma a gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) da kuma a gasar cin kofin kalubale na duniya (Confederations Cup) da suka gudana a kasar Koriya ta Kudu.

Wannan shi ne karo na farko da za a fara amfani da irin wannan na’ura a Afirka.