Minsitan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce nan da sati uku masu zuwa za a fara shimfida titin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano.
Amaechi ya sanar da haka ne a taron da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan ranar Alhamis.
- Da a biya kudin fansa gara ’yan bindiga sun kashe ni —Matar El-Rufai
- An tsinci gawar daliba a Jami’ar Bayero
“A cikin watan nan za mu fara aikin shimfida titin jirign kasa daga Kaduna zuwa Kano da na Fatakwal zuwa Maiduguri, sai kuma wanda ya tashi Kano zuwa Maradi, kuma duk kamfanin CCECC na kasar China ne zai awiatar,” inji shi.
Ya yi kira da a ci moriyar layin dogon Legas zuwa Ibadan yadda ya kamata, domin zai bunkasa tattalin arziki ya kuma saukake jigilar mutane da kaya a kan lokaci.
Sai dai ya nuna damuwa bisa jinkirin samun rancen kudin aikin titin jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Kaduna daga kasar China.
“Ba mu ji dadi ba gani har yanzu bankin China Exim Bank bai bayar da rancen kudin aikin Ibadan zuwa Kano ba, wanda muke son farawa da kammalawa da wuri.
“Muna fatar samun kudaden aikin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano domin a kammala da wuri a fara amfani da shi.
“Amma duk da haka mun yaba wa gwamantin China da ta ba mu rance mai sauki domin gina layin dogon daga tashar jirgin ruwa zuwa na jirgin kasa a Ibadan,” inji ministan.