✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dawo da sufurin jiragen kasa daga Legas zuwa Kano a watan Agusta

Jirgin zai rika barin Legas da yammacin Juma’a, ya isa Kano safiyar Lahadi.

Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta ce ranar 13 ga watan Agustan 2021 za ta dawo da sufurin jirgi daga Legas zuwa Kano.

Manajan Shiyya na hukumar mai kula da Arewacin Najeriya, Isma’il Adebiyi ne ya bayyana hakan ranar Lahadi, yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Zariya, Jihar Kaduna.

Ya ce jirgin zai rika barin Legas a kowacce ranar Juma’a da yamma, sannan ya isa Kano da safiyar ranar Lahadi.

Adebiyi ya kuma ce hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye wajen dawo da zirga-zirga tsakanin Kaduna zuwa Kafanchan da kuma Kaduna zuwa Kano kafin karshen watan na Agusta.

Ya kara da cewa za kuma su tashi sabbin taragai 1,000 domin karfafa harkar sufurin a cikin watanni biyu masu zuwa.

Manajan shiyyar ya ce sabbin taragan da za a gyara za a rika amfani da su ne a zirga-zirga tsakanin jihohin Arewacin Najeriya na Kano da Kaduna da Jigawa da Yobe da Katsina da kuma Zamfara.

Isma’il Adebiyi ya kuma ce jirgin da yake tashi daga Kano zuwa Nguru a Jihar Yobe na aiki yadda ya kamata, duk da yake shi ma suna nan za su kara yawan jigilar da yake yi ta hanyar dawo da taragan da aka jingine amfani da su saboda annobar COVID-19.

Kazalika, ya ce jirgin da ke tashi daga Kaduna zuwa Minna shi ma ya dawo da aiki kusan wata daya da ya wuce, kuma yana samun karuwar fasinjoji.

Jirgin dai na tashi ne a ranakun Lahadi da Litinin da kuma Alhamis, inda yake barin Minna da karfe 7:00 na safe sannan ya isa Kaduna da misalin karfe 2:00 na rana.