Gwamnatin Tarayya ta amince da sake dawo da karbar haraji daga motoci a manyan titunan da ke fadin kasar.
Hakan ya biyo amincewar da taron Majalisar Zartarwa ta tarayya ya yi a zamansa na ranar Laraba.
- Dalilin da na rubuta littafin ‘Garuruwan Karamar Hukumar Nasarawa’
- Gwamnoni sun fi Gwamnatin Tarayya barna – Baba-Ahmed
Sai dai harajin ba zai shafi motocin gwamnati ko sojoji da ma’aikatu da bubura da kekuna ba.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da ke ba da wannan tabbacin a jiya Laraba a Abuja.
A cewarsa, an dau matakin ne domin kara hanyoyin samun kudaden shiga.
Sannan ya ce dama tun a zamanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo a 2003 aka kirkiro wannan haraji, amma aka watsar don haka yanzu za a dawo da tsarin
Ministan ya ce kananan motoci za su ke biyan naira 200, manyan motoci kuma naira 500.