✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dage Gasar Zakarun Turai saboda cutar Kurona

Rahotanni da ke fitowa daga Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) sun ce akwai yiwuwar a dage wasannin Zakarun Kulob na Turai da kuma…

Rahotanni da ke fitowa daga Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) sun ce akwai yiwuwar a dage wasannin Zakarun Kulob na Turai da kuma Gasar Europa da zarar an kammala wasannin zagaye na biyu a makon gobe.

Yadda cutar take ci gaba da yaduwa a sassan duniya musamman a Nahiyar Turai ta sa hukumar daukar wasu matakai da suka hada da buga wasu wasanni ba tare da ’yan kallo ba.

Alal misali an yi wasan da Balancia ta Spain ta kece raini da Atalanta ta Italiya a ranar Talatar da ta wuce a Spain ba tare da ’yan kallo ba kamar yadda aka yi wasan Europa a tsakanin kulob din Inter Milan na Italiya da na Getafe da ke Spain a jiya Alhamis ba tare da ’yan kallo ba.  Haka abin yake a wasan da kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa ya yi da na Borussia Dortmund na Jamus a shekaranjiya Laraba a Gasar Zakarun Turai ba tare da ’yan kallo ba.

Sanarwar ta kara da cewa wasan da FC Barcelona za ta yi da kulob din Napoli na Italiya a ranar Larabar makon gobe ma za a yi shi ne ba tare da ’yan kallo ba.  Sannan a ranar Alhamis mai zuwa  za a karkare wasannin Europa da kungiyoyi 32 suke fafatawa a tsakaninsu inda daga nan ne hukumar za ta yi nazarin yaduwar cutar kuma ta dauki mataki na gaba.

Matakin da ake ganin hukumar za ta dauka shi ne na dage wasannin kwata fainal a Gasar Zakarun Turai da dage wasannin zagaye na biyu na Gasar Europa da zarar an kammala wasannin a makon gobe.