Mahukunta a Saudiyya sun sanya tarar riyal 1,000 ga duk wanda aka samu kan abin da suka kira kin sanya takunkumin rufe fuska domin dakile yaduwar annobar Coronavirus.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ce ta yi wannan gargadi da cewa a za ci tarar duk wadanda suka saba dokokin da aka shimfida na yaki da annobar cutar.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ma’aikatar tana cewa kin saka takunkumi ko wani kyalle domin rufe hanci da baki babban laifi ne wanda zai iya ja wa mutum ya biya tarar riyal 1,000.
BBC ya nakalto Ma’aikatar tana kuma bayyana cewa za a rubanya kudin idan mutum ya ci gaba da saba dokar har kudin su kai riyal dubu 100.
Tun a ranar Alhamis ta makon jiya ce Saudiyya ta dawo da dokokin dakile yaduwar cutar ciki har da sanya takunkumin rufe fuska da kuma bayar da tazara a masallatai a daidai lokacin da ake ci gaba fama da yaduwar sabon nau’in cutar na Omicron.