✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a ci gaba da kwaso ’yan Najeriya daga Sudan bayan tsaikon kwana 2

An yi alkawarin yau Asabar Za a bar wadanda suka makale a iyakar Sudan da Masar su wuce zuwa birnin Alkahira

Bayan kwana biyu da aka samu tsaiko wajen kwashe ’yan Najeriya da suka makale a yakin Sudan, Ofishin Jakadancin Najeriya da ke can ya sanar cewa a ranar Asabar zai ci gaba da kwaso su.

Tsaikon kwaso ’yan Najeriyar da aka samu tun ranar Alhamis ya haifar da ce-ce-ku-ce, kafin a yammacin ranar Juma’a ofishin ya sanar cewa zai ci gaba da kwasho su daga wasu jami’o’i biyu da ke Khartoum, babban birnin Sudan.

Wannan sanarwar dai na zuwa ne bayan zargin da daliban Najeriya da ke Sudan suka yi cewa jami’an ofishin jakadancin sun kwashe iyalansu sun tsere daga kasar da ke fama da yaki, suka bar su.

Daliban sun yi zargin cewa jami’an sun tsere sun bar su ne kafin karewar wa’adin ranar Juma’a da bangarorin da ke yaki da juna a Sudan suka amince su tsagaita wuta; amma a ranar Juma’a suka kara tsawaita wa’adin.

Sun kuma bayyana cewa ’yan uwansu dalibai da sauran ’yan Najeriya da aka fara kwashewa daga Khartoum sun makale a iyakar Sudan da kasar Masar  saboda rashin takardun biza.

Wata majiya daga wasu iyayen daliban da hakan ta shafa ta yi zargin cewa jami’an ofishin jakadancin Najeriya da ke alhakin nema musu bizar shiga kasar Masar sun riga sun bar Khartoum sun tafi birnin Alkahira na kasar Masar.

Sai dai daga bisani majiyar ta ce an yi wa wadanda suka makale a iyakar kasashen biyu alkawarin za a bari su wuce zuwa birnin Alkahira a ranar Asabar.