Gwamnatin Kaduna ta sanya 10 ga watan Agusta a matsayin ranar bude makarantu ga dalibai masu kammala karatun sakandare.
Kwamishinan Ilimin Jihar Kaduna, Shehu Usman Muhammad ya ce ba a yarda wata makaranta mai zaman kanta ko ta gwamnati ta koma ba kafin ranar.
“Shugabannin makarantu su tabbatar da kiyaye dukkanin dokoki da suka hada da rage sa’o’in aiki zuwa awa hurhudu a kowane zango, bayar da tazara a cikin aji da dakunan gwaje-gwaje da dakunan karatu da sauransu”, inji sanarwar da ya fitar ranar Litinin.
Daliban za su fara rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC ce daga ranar 17 ga watan na Agusta.
Kwamishinan ya ce nan gaba za a sanar da ranakun bude makarantun ga sauran dalibai
Ya ce gwamnatin jihar ta kuma dukufa wajen daukar matakan da za su kai ga bude makarantunta, ta hanyar yin feshin magani da kuma samar da kayan wanke hannu.
Sauran su ne samar kayan auna zafin jiki da takunkumi da kuma sinadaran wanke hannu ga ma’aikata da dalibai a makarantun.
Bullar cutar COVID-19 a Najeriya ta tilasta rufe makarantu tun a watan Maris.
A cikin watan Yuli Gwamantin Tarayya ta sanar da bude makarantu ga dalibai masu jararbawar WAEC a ranar 4 ga Agusta.