✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a bude makarantu ranar 18 ga Janairu —Gwamantin Tarayya

Rashin kiyaye matakan kariyar COVID-19 zai sa a dawo da dokar hana fita

Gwamnatin Tarayya ta ce har yanzu ba ta sauya ranar bude makarantu daga ranar 18 ga watan Janairun 2021 ba.

Kwamitin Yaki da cutar COVID-19 da Shugaban Kasa ya kafa ya ce babu sauyi a ranar bude makarantun har sai idan Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar da sabanin hakan.

Shugaban Kwamitin, Dokta Sani Aliyu ne ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a wani shirin gidan talabijin a ranar Talata a Abuja.

A ranar Litinin, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ce Gwamnatin Tarayya ta tsayar da ranar 18 ga Janairu, 2021 domin bude makarantun ne duba da yadda ake samun karuwar masu kamuwa da kuma masu rasuwa sakamakon cutar COVID-19 a Najeriya.

A nasa bangaren, Dokta Sani ya ce yanayin yadda ’yan Najeriya suka kiyaye matakanan kariyar cutar ce ne zai yi alkalanci game da yiwuwar sake sanya dokar hana fita.

Ya ce, “Ba Kwamitin ba ne zai yanke hukuncin sanya dokar hana fita ba, amma dabi’ar mutane ce za a duba idan aka tashi sanya dokokin.”