✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a ba taurarin Kannywood guda 7 lambar yabo a Landan

Wani Kamfanin jarida na birnin Landan mai suna African voice ya zabi taurarin kannywood guda bakwai  domin ba su lambar yabo dangane da  qwazon da…

Wani Kamfanin jarida na birnin Landan mai suna African voice ya zabi taurarin kannywood guda bakwai  domin ba su lambar yabo dangane da  qwazon da suka nuna a masana’antar ta kannywood. Bikin bada lambar yabon za a yishi ne a ranar hudu  ga watan Nuwamba , 2017.

Taurarin da zasu amshi lambar yabon sun hada da Nafisa Abdullahi, Hafsat Ahmed, Halima Atete, Ramadan Booth, Sani Ahmad Yaro, Kamal Alkali da Hamisu Lamido Iyantama.

Lambar yabon zai kasance a vangarori uku: ‘yan wasa, bada umarni  da kuma shiryawa.