✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a aika da Rigobert Song Faransa bayan ya farfado daga sumar kwana biyu

A ranar Talatar da ta wuce ne iyalan tsohon dan kwallon Kamaru Rigobert Song suka yanke shawarar aikawa da shi Faransa don ci gaba da…

A ranar Talatar da ta wuce ne iyalan tsohon dan kwallon Kamaru Rigobert Song suka yanke shawarar aikawa da shi Faransa don ci gaba da samun magani bayan ya farfado daga sumar kwana biyu. Song wanda yanzu haka shi ne kocin kungiyar kwallon kafa ta Chadi, ya yanke jiki ya fadi ne a gidansa da ke Kamaru a ranar Lahadin da ta wuce.
Song, wanda kawu ne ga dan kwallon Arsenal na Ingila Aled Song ya rike kyaftin a kungiyar kwallon kafa ta Kamaru a lokacin da yake kwallo.
Rahotanni sun nuna shahrarren dan kwallon Kamaru Samuel Eto’o yana daga cikin ’yan kwallon da za su tallafa wa Song don ganin an kai shi wani asibiti da ke Faransa kafin karshen wannan mako. Rigobert Song kafin ya daina kwallo ya yi wasa a kulob da dama da suka hada da  Liberpool da West Ham United da ke Ingila da Galatassaray na Turkiyya da sauransu.