Hukumomi sun tabbatar da mutuwar ƙananan yara 66 a sakamakon yunwa a yankin Gaza.
Yaran sun mutu a yayin da sojojin Isra’ila ke ci gaba da hana shigar da madarar yara da sauran kayan abinci da sauran kayan jinƙai da ake buƙata domin ceto rayuka zuwa Gaza.
Mutuwar yaran ta zo ne a daidai lokacin da hukumomin Gaza suka sanar cewa sojojin Isra’ila sun kashe wasu Palasdinawa 34.
Jami’an lafiya a Asibitin Al-Shifa da ke Gaza sun bayyana cewa an kawo gawarwakin wasu mutum 12 da sojojin Isra’ila suka kashe a filin wasa da Palasdinawa ke zaman mafaka, da wasu takwas da aka kashe a wani gida.
- ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’
- Yadda aka yi jana’izar kwamandojin Iran da Isra’ila ta kashe
Ofishin yaɗa labarai na hukumomin Gaza ya bayyana cewa ana matuƙar buƙatar kayan abincin domin ceto rayuwar musamman ƙananan yara da gajiyayyu da marasa lafiya.
Sanarwar Hukumar ta ce, “laifin yaƙi ne da tauye haƙƙin ɗan Adam ne abin da Isra’ila ke yi na amfani da salon hana faren hula samun abinci a matsayin makami.
“Wannan ya saɓa da yarjejeniyar Geneva da kuma dokokin ayyukan jinƙai na duniya.”