✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yin sadaka a asirce

Daga Hudubar Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-HusainMasallacin Sharif Ibrahim Saleh, Gwange, Maiduguri Huduba ta Biyu:Hamdala da shahada da salati: Bayan haka, ya ’yan uwa muminai!…

 Sheikh Sharif Ibrahim SalehDaga Hudubar Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Husain
Masallacin Sharif Ibrahim Saleh, Gwange, Maiduguri

Huduba ta Biyu:
Hamdala da shahada da salati:

Bayan haka, ya ’yan uwa muminai! Wannan bangare da muka yi magana a kansa, ya bijiro ne domin yin gini kan abubuwan da suka wuce mu ko muke cikinsu a yanzu. Amma batun da muke son yin magana a kansa shi ne na yin sadaka a asirce, ko mu ce sadakar da mutum yake boye ta sai don Allah shi kadai ya sani sai wanda ya yi wa sadakar.
A cikin wani Hadisi daga Hadisan Manzon Allah (SAW) ya ambaci cewa: “Mutum uku Allah Yana sonsu, uku kuma Allah Yana kinsu.” Sai ya ambaci wadanda Allah Yake so, daya daga cikinsu shi ne: “Wani mutum ya tsaya a tsakanin jama’a ta Musulmi sai ya roke su domin Allah.” Bai roke su domin dangantakar da ke tsakaninsu ba. Sai wani mutum daga cikinsu ya tsaya, ya yi masa kyauta babu wanda ya sani daga shi kansa sai wanda ya ba shi da kuma Allah Madaukaki.” Wannan mutum Allah Yana sonsa. “Sai mutanen da suka yi tafiya cikin dare,” wannan tafiya tasu domin aikin alheri ne. Imma domin jihadi ko kasuwanci don jawo alheri ga kasashen Musulmi, ko domin kai wani sako da Manzon Allah (SAW) ya aike su. “Suka yi tafiya cikin dare har ya zam barcin ya zame musu dole, sai suka yi barcin. Amma wani mutum – daga cikinsu – ya tashi yana bauta Min (Allah) yana fatar rahamaTa, yana kiraNa yana yin addu’a gare Ni, yana karanta ayoyiNa.” Wannan shi ne mutum na biyu daga cikin wadanda Allah Yake so. “Sai mutanen da suka fita kai hari suka hadu da abokan gabarsu, suka kora su. Sai wani daga cikinsu ya fita ya fuskanci abokan gaba gadan-gadan imma ya samu shahada ko a yi masa budi.” Wadannan nau’o’in mutum uku dukkansu ladansu yana wurin Allah, kuma dukkansu Allah Madaukaki Ya ambace su a cikin masoyanSa.
“Mutum uku da Allah Yake kinsu Yake fushi da su, su ne: Tsoho mazinaci” Shi ne tsohon da yawan shekarunsa bai kange shi daga kazantar zina ba. Zina ita ce mafi munin dabi’a a tsakanin jama’a. “Sai fakiri (talaka) mai girman kai.” Fakiri ne, amma yana nuna shi mawadaci ne, yana nuna yana da abin da ba ya da shi. Yana nuna shi ba ya bukatar komai, alhali bai mallaki komai ba. Kaitonsa ina ma ya takaita a kan wannan ya yi da’a ga Ubangijinsa ya yi kwadayi a wurin Ubangijinsa. Maimakon haka idan ya kebanta da abin da Allah bai so, sai ya auka a cikinsa. To, fakiri mai girman kai Allah Yana kyamarsa. Amma idan ya zamo fakiri mai kamun kai ne wannan babu laifi. “Sai mawadaci azzalumi.” Shi ne na uku.
Ga nassin Hadisin: “Mutum uku Allah Yana sonsu, mutum uku kuma Allah Yana kinsu. Amma wadanda Yake sonsu, (su ne) mutanen da wani mutum ya zo musu ya roke su domin Allah. Bai roke su domin wata dangantaka da ke tsakaninsu ba. Suka hana shi, sai mutum daya ya saura a bayansu, sai ya ba shi a asirce, ba wanda ya san ya bayar sai Allah da kuma wanda aka ba shi da shi wanda ya bayar. Sai mutanen da suka yi tafiya cikin dare har barci ya rika fisgarsu ya zamo barcin ne mafi soyuwa a gare su daga komai, sai suka kwanta. Sai wani daga cikinsu ya tashi yana bauta Min, yana karanta ayoyiNa. Sai mutumin da ke cikin masu kai hari suka hadu da abokan gaba, suka kora su, sai ya bi su a baya har aka kashe shi ko aka yi masa budi. Mutum ukun da Allah Yake ki su ne: Tsoho mazinaci da fakiri mai girman kai da mawadaci azzalumi.” Abu Dawuda da Ibnu Khuzaima da Nisa’i da Tirmizi da Ibnu Hibban a cikin sahihinsa suka ruwaito. Sai dai Ibnu Hibban ya fadi a karshensa cewa: “Yana fushi da tsoho mazinaci da marowaci da mai girman kai.” Kuma Hakim ya ruwaito shi a cikin Almustadrak daga Abu Zarri.
Mawadaci azzalumi: Zaluncin da ke aukuwa a kasarmu a yau, har abada bai zai auku daga fakirai ba. Har abada ba zai auku daga masu rauni ba. Har abada ba zai auku daga yaku bayi ko kananan ’yan kasuwa ba. Zaluncin yana gudana ne a tsakanin mutane a nan kasar daga bangaren mawadatan kasar! Na ce mawadatan kasar. Su wane ne mawadatan kasar?
Ya kasance a baya kafin bayyanar fetur, mutane suna noma, kuma Allah Madaukaki Yana sanya musu albarka a ciki sosai, sai su wayi gari mawadata ta hanyar noma da kiwo. Mutane sun kasance suna yin sana’o’i manya da kanana, sai Allah Ya wadata su ta haka, Ya sanya musu albarka. Bayan bayyanan fetur, sai muka koma dogaro kan fetur, aka wayi gari mawadata ko masu kudi a cikin mutane su ne manyan ma’aikata kawai. Lokacin da siyasa ta bayyana, sai ma’aikata da sauran mutane suka zamo abu daya. Dukiya ko wadata ta tattare a hannun wadanda aka sani da siyasa, ’yan siyasa su ne masu kudi ko mawadata!   
Idan haka lamarin yake, dan siyasa ana zabensa a wannan kasa da sauran kasashen duniya duka ne domin ya cika alkawarinsa. Amma sai ya ci wannan amana ta hanyar juya bayansa ga addini da juya baya ga fakirai da wadanda suka yi masa wahala wajen zabensa da wadanda suka tsaya masa ya kai kan wannan matsayi. To yanzu wannan dukiya tana juyawa ne a hannun wadannan, alhali dukiyar ta dukkan jama’a ce. Dukiyar ta dukkan jama’a ce, bai halatta wasu kalilan su yi rub-da ciki kanta ba, su hana sauran al’umma.
Mun san cewa lallai Allah ne Yake mallakar komai, mulki sammai da kasa na Allah ne. Mun san haka, sai dai Allah Yana da hukunci Yana da shari’a. Kuma Ya hukunta sanya wannan dukiya a duniya, ga wanda yake zaune a yankin da muke kira daula. Daula tana nufin taron jama’a, tana nufin yankin kasa, tana nufin hukumar da take shugabancin wannan jama’a take hukunta wannan yanki na kasa. Wannan iko shi masu zabe suke ba wadanda suka zaba ta hanyar jefa musu kuri’a da zabensu a mukamai daban-daban tun daga majalisun kananan hukumomi da na jihohi da na tarayya da bangaren shari’a da na zartarwa da kuma na Shugaban kasa.  
Irin wannan magana tana da wuyar fadi, tana da wahala a wurin wasu mutane. Ba za ka fade ta ba, matukar kana son masu dukiya ko masu kudi su so ka. Amma dai ita ce gaskiyar magana! Muna gaya musu su koma ga gaskiya, su canja, su sake halayensu… Domin Allah ba Ya canja halin da mutane suke ciki, sai sun canja zukatansu. “Lallai Alah ba Ya canja abin da yake ga mutane sai sun canja abin da yake zukatansu.” (k:13:11).
Idan haka ne kuma muna nufin gyara, tilas mu yi haka, idan kuma ba haka ba, karshen lamarin zai kasance mummuna, yanzu ko nan gaba.
Muna magana ne kan sadaka a asirce, mun tabo wadannan abubuwa ne, saboda mun ambaci mawadaci azzalumi.
A cikin wani Hadisi na Anas bin Malik (RA) ya ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Allah lokacin da Ya halicci kasa, an sanya ta tana yayyankewa tana motsawa – tana jujjuyawa ba ta tsaya ko ta nastu ba – Ya karfafa ta da duwatsu sai ta natsu. Sai mala’iku suka ji mamaki kan karfin duwatsu, suka ce: “Ya Ubangijinmu! Shin Ka halicci wani abu da ya fi duwatsu karfi?” Ya ce: “Na’am. karfe.” Suka ce: “Shin Ka halicci wani abu da ya fi karfe karfi?” Ya ce: “Wuta.” Suka ce: “Shin Ka halicci wani abu da ya fi wuta karfi?” Ya ce: “Ruwa.” Suka ce: “Shin Ka halicci wani abu da ya fi ruwa karfi? Ya ce: “Iska.” Suka ce: “Shin Ka halicci wani abu da ya fi iska karfi?” Ya ce: “Idan dan Adam ya yi sadaka da hannunsa na dama ya boye ta daga hagunansa.” Tirmizi da Baihaki ya ruwaito.
Ke nan manufa ba sadakar kanta ba ce, manufa yin aiki na gaskiya da kake yinsa domin neman yardar Allah. Lokacin da kake sadaka a asirce ma’anarta: Kai ba ka neman wanda ka yi wa sadakar ya yabe ka, ko ya yi maka godiya ko ya ambace ka a cikin jama’a ko wani wuri. Wannan daya ke nan.  
Sannan lallai kai ba za ka dogara kan wannan sadaka ba ka ce, tunda ina sadaka a boye zan shiga Aljanna! A’a, kai idan ka aikata wannan ibada domin Allah Madaukaki da kwatanta umarninSa, sai ka bar tsirarka da shigarka Aljanna ya zamo al’amari ne da ke hannun Allah Madaukaki. Allah ne Mafi alherin Wanda Yake kyautata wa wanda ya kyautata, Ya ce: “Shin kyautatawa na da wani sakamako ne face kyautatawa?” (k:56:60).