✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yi amfani da abin da ka samu

Barka da warhaka Manyan Gobe Fatan alheri a gare ku, ina fata kuna mayar da hankali kan karatu. A yau na kawo muku labarin ‘Yi…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Fatan alheri a gare ku, ina fata kuna mayar da hankali kan karatu. A yau na kawo muku labarin ‘Yi amfani da abin da ka samu’. Wannan labarin na koya wa Manyan Gobe su yi amfani da abin da suka samu idan kuma ba haka ba suna kallon ruwa, sai kwado ya yi musu kafa.
A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Yi amfani da abin da ka samu

A wani zamani da ya wuce  an yi wani manomi wanda yake da bijimai guda uku. Akwai wani saurayi wanda yake son ya auri ‘yarsa. Manomin kuma ya yi alkawarin  zai ba da ‘yarsa ga wanda ya cancanta, cancarta kuwa ita ce idan mutum ya iya kama babban bijimin da ya fi girma a cikin shanunsa, to zai samu damar auren ‘yar manomi.
Da manomi ya bude wurin da yake kiwon shanunsa, sai bijimai suka fara fitowa a guje. Na farkon bijimin ya fi girma. Na biyun kuma bai kai na farkon girma ba, na ukun ne karami a cikinsu. A maimakon saurayin ya kama na farkon, sai  ya tsaya jiran sauran shanun su fito. Daga karshe dai bai samu damar kama babban bijimin ba sai wani marar kiba. Hakan kuma ya sa aka hana shi auren ‘yar manomin.
Wannan labarin na koya wa Manyan Gobe  su yi amfani da abin da suka samu, domin da saurayin ya kama na farkon da ya samu sa’ar kama babban bijimin.