✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yayin da Rabiu Ibrahim ya koma KAA Gent

dan wasan Najeriya Rabi’u Ibrahim wanda ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta AS Trencin da ke kasar Slobakia ya koma kungiyar KAA Gent dake…

dan wasan Najeriya Rabi’u Ibrahim wanda ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta AS Trencin da ke kasar Slobakia ya koma kungiyar KAA Gent dake kasar Bejum.
dan wasan, yana daya daga  cikin ‘yan wasan kasa da shekara 17 da suka lashe gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekara 17 a kasar Koriya ta Kudu a shekarar 2007. Sannan kuma zai hadu da Simon Moses a kungiyar ta KAA Gent wanda shi ma ya buga wa kungiyar AS Trencin kafin ya koma KAA Gent a shekara 2014.
dan wasan ya ce “ da gaske ina kasar Beljum yanzu haka, ina matukar jin dadi da na samu damar buga wa babban kungiya kamar ta KAA Gent, sannan  ina godiya ga daukacin magoya bayan kungiyar AS Trencin domin sun nuna min kauna a lokacin da nake kungiyar, ba zan taba mantawa da su ba.
Ya kara da cewa” ina sa ran idan na nuna kwazo a kasar Beljiyam zai taimake ni wurin samun damar a kara kirana domin in cigaba da buga wa Najeriya kwallo.
Rabi’u Ibrahim dai ya buga wa Najeriya wasa sau biyar a matakin Super Eagles.