Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila ta fitar da jadawalin gasar cin kofin kalubale na kasar da aka fi sani da (FA).
kungiyoyi uku ne suka tsallake zuwa wannan mataki da suka hada da Crystal Palace da Watford da kuma Eberton. Sai dai kulob na hudu zai fito ne a tsakanin kulob din Manchester United ko na West Ham United da za su sake karawa a wasa na biyu bayan sun yi kunnen doki 1-1 a wasan farko.
Jadawalin ya nuna kulob din Crystal Palace zai hadu ne da na Watford a ranar 23 ga watan gobe (Afrilu) yayin da Eberton kuma za ta kece raini ne da kulob din Manchester United ko na West Ham United.
Idan za a tuna, a ranar Lahadin da ta wuce ne kulob din Manchester United ya tashi kunnen doki ci 1-1 da na West Ham United al’amarin da ta sa za su sake haduwa a wasa karo na biyu nan gaba kadan. Don haka kulob din Eberton dai yana jiran daya daga cikin kulob din Man U ko na West Ham a wasan semi fainal.
…Yayin da aka fitar da jadawalin gasar cin kofin kalubale (FA) na Ingila
Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila ta fitar da jadawalin gasar cin kofin kalubale na kasar da aka fi sani da (FA).kungiyoyi uku ne suka…