Hannatu Musa, daya daga cikin matan Chibok din da sojoji suka ceto ta ce ’ya’yanta guda biyu da ta haifa a sansanin Boko Haram sun taba shafe kwana 40 babu abin da suke ci sai ganyayyaki.
Ta ce yanzu babban abin da ya fi damunta shi ne lafiyar ’ya’yanta nata guda biyu, kamar yadda ta shaida wa manema labarai a zantawarta da su a a hedkwatar rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
“Ni da ’ya’yana mun yi kusan wata biyu muna cin ganye kafin na tsira,” inji Hannatu.
Ita kuwa Kauna Luka, wacce aka ceto tare da Hannaru, ta ce sam ba ta da sha’awar ci gaba da karatunta, saboda tsoron ’yan ta’addan Boko Haram su sake sace ta a karo na biyu.
ta ce, ita a radin kan ta tafi son Gwamnatin Tarayya da na jihohi su taimaka mata da danginta.
Ta ce ta fi so ta tsunduma sana’ar dinki don sake gina rayuwarta sabanin a baya da aka gurbata mata ita.
“Ba na son komawa makaranta; ina fargabar ’yan ta’addan Boko Haram su dawo su yi garkuwa da ni,” inji Kauna, wacce ita ce ta shida daga a cikin ’ya’yan da iyayenta suka haifa su 10.
Mai shekara 25, Kauna, wacce ta samu ’yanci da ’yarta dai ba ita kadai ba ce take sha’awar barin makaranta saboda tsoron sake sace su.
Kamar yadda rahoton ya nuna duka Kauna Luka da Hannatu Musa da aka ceto na daga cikin nasarorin baya-bayan nan na nasarar da sojojin Najeriya suka yi a kan sansanonin ‘yan ta’addar Boko Haram.
Kwamandan rundunar ta Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, yayin da yake bayyana wasu nasarorin da rundunar tasu ta samu a wani taron manema labarai, ya bayyana cewa dabarunsa na yaki da Boko Haram ne suka taimaka wajen ceto matan tare da wasu da aka kubutar daga zaman talala.
“Sojojinmu yanzu suna shiga kowane yanki da sansanonin ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, wadda hakan kan ba su dama [su ’yan matan Chibok da sauran wadanda aka sace] su fito daga hannunsu.
“Za mu ci gaba da matsawa har sai duk ’yan matan Chibok da sauran wadanda aka sace sun kubuta daga hannun wadannan ’yan ta’addan,” inji Janar Musa.
Matan biyu sun tsere ne daga sansanin ’yan ta’addan na Boko Haram na Gazuwa, inda suka bi ta hanyar daji kafin daga bisani sojoji su kubutar da su a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.