✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya’yan itacen da ke gyara fata

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon na kawo miki nau’ikan ’ya’yan itacen da ke gyara fata. Ina fata za…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon na kawo miki nau’ikan ’ya’yan itacen da ke gyara fata. Ina fata za ki juri cin su don samu fata mai sheki da santsi.

Dankali: Dankali na dunshe da sinadarin bitamin A, wannan sinadari na fada da kwayar cutar da ke haifar da kuraje.Yana dauke da sinadarin bitamin C da ki magance kuraje da kuma tabon fata, don haka idan kika rika cin dankali za ki samu fata mai sheki da kuma kyawu.
. ’Ya’yan kabewa: Tana dauke da sinadarin Zinc da ke taimakawa wajen samar da halittar kwayoyin halittar fata, sannan yana taimakawa wajen sarrafa Protein da ke jikin fata. ’ya’yan kabewa na samar da mai a jikin fata, sannan ta inganta launin fata.
. Tuffa: Na kunshe da sinadarin bitamin C da ke kara karfin fata da kuma kare fata daga saurin tsufa, sannan tana taimaka wa kwayoyin halittar fata wajen yaki da duk kwayoyin cuta.
. Karas: Idan har kina so ki rika kasancewa mai karancin shekaru sai ki rika cin karas, amma ki rika hada shi da ganyayyanki. Karas na dauke da sinadarin beta carotene da bitamin A.
. Inibi: Idan kika hada inibi da zuma, ko fiya da yogut za ki samu fata mai inganci, za su rika kare fatarki daga zafin rana. Inibi na dauke da sinadarin Malic acid.
. Lemon Tsami: Na dauke da sinadarin bitamin C, wanda hakan ke taimakawa wajen samar da sinadaran Protein da ke fata. Don haka shan lemon tsami da kuma shafa ruwansa a kan fata na magance kuraje, za a kuma samu fata mai damshi da kuma santsi.
. Tumatir: Na dauke da sinadarin lycopene da ke taimakawa wajen kare fata ta ciki da kuma ta waje daga zafin rana. Idan kika shafa ruwan tumatir a kan kuraje zai sanya su bushe.
. Alayyahu: Na dauke da sinadarin da ke taimaka wa fata, yakan hana ta jemewa ko yaushi, sannan yana dauke da sinadarin da ke fitar da duk wata guba da ke cikin fata.