Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta ce akwai yiwuwar yawan talakawa ya karu zuwa miliyan 109 nan da karshen shekarar 2022.
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, wacce ta bayyana hakan ta ce sabbin mutum miliyan 11 na iya fada wa kangin talauci a cikin shekarar sakamakon annobar COVID-19.
Ta yi wadannan kalaman ne a Abuja, a ci gaba da taron da ake yi kan annobar COVID-19 mai taken ‘Fadan karshe wajen yaki, tare da murmurewa daga annobar COVID-19’.
Ministar, wacce ta sami wakilcin Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi, Ben Akabueze, ta ce akalla mutum miliyan biyu ne suka fada talauci a 2020 saboda yadda yawan jama’a ya zarce karfin tattalin arzikin kasa.
Ta kuma ce annobar ta COVID-19 da kuma karyewar tattalin arziki sun kara yawan wasu matalautan da kimanin miliyan 6.6, lamarin da ya kawo adadin zuwa miliyan 8.6 a cikin shekarar kawai.
“Hakan na nuni da yiwuwar karuwar talakawa a Najeriya daga miliyan 90 a 2020 zuwa miliyan 109 a 2022,” inji Zainab.
Ta alakanta kalubalen da yawan karuwar ayyukan da ba su da tabbas, wadanda ta ce su ma sun dada jefa jama’a cikin kangin talaucin.