✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yawan mutanen duniya zai kai biliyan 8 kafin karshen 2022 – MDD

Sai dai majalisar ta ce ana samun karancin haihuwa a duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi harsashen cewa adadin mutanen duniya zai kai biliyan takwas kafin nan da karshen wannan shekarar ta 2022.

Sai dai harsashen, wanda ke zuwa a Ranar Kidaya ta Duniya wacce ake bikinta wannan Litinin din ya ce karuwar mutanen duniyar na tafiyar hawainiya a ’yan shekarun nan.

Rahoton ya ce, “A shekarar 2020, adadin karuwar mutanen duniya ya ragu da kaso daya cikin 100 a karo na farko tun shekarar 1950.”

A cewar Daraktan Sashen Kidaya na Majalisar, John Wilmoth, duk da banbance-banbancen da ake samu a sassan duniya daban-daban, hakan zai samar da muhimmiyar dama ga kasashe masu tasowa.

Ya ce ban da taimakawa wajen yaki da talauci da yunwa, kasashen za su sami alfanu a wajen ilimi, sakamakon karancin yaran na nufin wadanda ake da su za su rika samun cikakkiyar kulawa.

Rahoton ya kuma ce karancin haihuwa na nufin za a sami yawan tsofaffi wadanda za su rika bukatar tallafi.

Kazalika, rahoton ya gano cewa karin kasashe masu karfin tattalin arziki za su yi fama da karancin jama’a kamar yadda a yanzu haka Japan take fama da shi, lamarin da zai tilasta wa kasashe irinsu Jamus su dogara da ’yan ci-rani don yi musu wasu ayyukan.

Sai dai duk da wannan harsashen, rahoton ya ce yana sa ran yawan mutanen duniyar ya kai biliyan takwas nan da ranar 15 ga watan Nuwamban bana.

Masana dai sun yi harsashen cewa zuwa nan da shekara ta 2023, adadin mutanen zai kai biliyan takwas da rabi, yayin da kuma nan da 2080 za su kai biliyan 10 da miliyan 400, inda za su ci gaba da zama a haka har zuwa shekara ta 2100.

(NAN)