✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutuwar sama da mutum 150 a kwana 3 ta sa fargaba a Kano

Al’ummar birnin Kano sun shiga zaman zulumi da fargaba sakamakon yawan mace-macen da ake yi a daidai lokacin da ake zaman kulle saboda barkewar annobar…

Al’ummar birnin Kano sun shiga zaman zulumi da fargaba sakamakon yawan mace-macen da ake yi a daidai lokacin da ake zaman kulle saboda barkewar annobar coronavirus.

Yayin wata ziyara da Aminiya ta kai makabartar Dandolo da ke Goron Dutse ta gano cewa a kwanaki uku an binne gawa fiye da 70.

Malam Bashir Muhammad, wanda aka fi sani da Mai Sana’a, shi ne shugaban masu kula da makabartar ta Dandolo kuma ya ce yadda ake kai gawarwaki abin dubawa ne.

“Yadda ake mace-mace ya saba abin da aka saba gani a baya; wanda bai fi a kawo gawa 10 ba”, inji shi.

Abin ya saba al’ada

A makabartar Abatuwa ma Aminiya ta gano cewa a tsakanin ranakun Asabar da Lahadi an binne fiye da mutane 70.

Haka abin yake a wasu makabartun da suka hada da ta Kuka Bulukiya da ta Gwale da kuma ta Court Road, inda binciken Aminiya ya gano cewa a kowacce makabarta akan binne akalla gawa 16 zuwa 20 a kullum.

Aminiya ta kuma zaga wasu daga cikin unguwannin kwaryar birnin Kano inda aka samu rasuwar mutane masu tarin yawa.

A unguwannin Zangon Barebari da Zage zuwa Dukawa an samu rasuwar akalla mutane 24 a ranar Asabar kamar yadda wani mazaunin yankin Nazifi Muhammad Dukawa ya tabbatar.

A unguwannin Mandawari da Marmara zuwa Kwanar Goda da Sheshe an samu akalla  mutane 35 kamar yadda wani mazaunin yankin Bashir Aminu Garba ya shaida wa Aminiya.

‘Wannan abu ya zama annoba’

Malam Baba Adamu shi ne mai unguwar Sheshe, ya kuma bayyana yawan mace-macen da ake yi a birnin a matsayin annoba.

“Wannan abu ya zama annoba domin mun yi jana’izar wata mata mun tafi kai ta kafin mu dawo muka tarar da wasu uku sun rasu, don haka muka fito da su muka yi musu sallah gaba daya. Abin fa sai addua”, inji mai unguwar.

Wani abin lura game da wannan lamari kuma shi ne galibin wadanda suka rasun mutane ne da suka manyanta.

Ra’ayin liktoci

Aminiya ta tattauna da Dokta Aminu Muhammad, wani likita a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, wanda ya bayyana cewa a duk lokacin da yanayin zafi ya shigo akan samu barkewar cututtuka musamman zazzabin cizon sauro.

“Yanzu a asibiti abin da muke fama da shi ke nan—a ko yaushe kika zo za ki tarar da marasa lafiya masu yawa kuma idan kika bincika za ki ga yawancinsu zazzabin maleriya ke damunsu”, inji likitan.

Ita kuwa Dokta Binta Jibrin, wata likita a Asibitin Hasiya Bayero, cewa ta yi duk da a lokacin zafi ana samun karuwar cututtukan da ke da alaka da zazzabin cizon sauro, ba dole ba ne a ce duk mutanen da suke mutuwa sun mutu ne sanadiyyar wannan cutar, musamman ma da aka ce wadanda abin ya fi shafa tsofaffi ne.

“Kin san tsofaffi ba sa rasa wasu cututtuka a tattare da su—abin da ake kira terminal illness–to kin ga kuwa ba za a ce sun mutu ne don cutar cizon sauro kadai ba ko da kuwa sun kamu da cutar.”

Hukuma na bincike

A wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa-hannun Jami’arta ta Hulda da Jama’a, Hadiza Mustapha Namadi, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike a kan musababbin yawan mace-macen.

Tun da farko dai a shafinta na Twitter, ma’aikatar ta yi kira ne ga jama’a da su yi watsi da wannan “jita-jita”, tana cewa “Kwamitin Cika Aiki kan COVID-19 ya aiwatar da tsarin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na ’yan rahoto a tsakanin al’umma wadanda za su rika kawo labarin mutuwa da dalilan mutuwar, sannan ya tura jami’ai zuwa dukkan makabartu don su kidaya gawarwakin da ake kawowa a kullum…”

Yanzu dai al’ummar Kano za ta saurari sakamakon binciken da ma’aikatar lafiyar ta ce za ta gudanar don jin hakikanin musabbabin wadannan mace-mace.