✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yawan karbar haraji na ci mana tuwo a kwarya’

Shugaban kungiyar Masu Fataucin Dabbobi ta kasa Alhaji Mustapha Ali Kwanar dangora ya ce  an samu ci gaba ta fannin fataucin dabbobi daga arewacin kasar…

Shugaban kungiyar Masu Fataucin Dabbobi ta kasa Alhaji Mustapha Ali Kwanar dangora ya ce  an samu ci gaba ta fannin fataucin dabbobi daga arewacin kasar nan zuwa kudanci saboda tsaron da aka samu da zaman lafiya, sai dai ya yi korafi game da yawan karbar haraji da ake yi daga hannunsu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Wace gudummawa sana’ar ku ke bayarwa wajen bunkasa tattalin arziki?
Ina so al’umma su gane cewa sana’ar mu tana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da samar da ayyukan yi ga al’umma ta fannoni daban-daban.
Hakazalika, idan ka duba harkar fataucin dabbobi za ka fahimci cewa akwai rufin asiri a cikin ta kwarai da gaske musamman ganin cewa sana’ace wadda ta kunshi saye da sayar wa ta dabbobi daga sashen arewacin kasar nan zuwa kudanci.
Don haka akwai gudummawa gagaruma da muke bayar wa wajen bunkasa tattalin arzikin wannan kasa, ta hanyar sana’ar mu ta fataucin dabbobi, kana muna samar da karin hanyoyi na samar da ayyukan yi a kasa duba da irin yawan da masu wannan harka ta fataucin dabbobi ke ciki domin dogaro da kai.
Aminiya: Wane kalubale kuke fuskanta?
Babu shakka cikin  harkokin  kasuwanci irin namu  akwai kalubale walau na cikin gida ko kuma kalubale tsakanin abokan hulda,  ko kuma kalubale tsakanin mu da hukumomi, amma Allah cikin ikonsa muna kokari matuka wajen  samun masalaha kan kowace irin matsala da take taso mana a kungiyarmu,  don haka ina kara tabbatar wa da jama’a cewa kungiyarmu tana aiki ne da murya guda domin ganin al’amura suna tafiya cikin nasara tun shekaru masu tsawo.
Aminiya: Ta ya ya kuke hada kawunan ’ya’yan kungiyarku?
Akwai hanyoyi masu tarin yawa da muke bi wajen hada kawunan mambobin kungiyarmu ta masu fataucin dabbobi. Kuma Alhamdulillahi muna aiki ne da murya guda kamar yadda na bayyana tun farko ba mu da wata matsala ta cikin gida kuma kowa yana harkokinsa bisa  tsari da bin dokokin kungiya kamar yadda ake bukata.
Muna kai dabbobi kusan dukkan sassan wannan kasar, sannan muna da kyakkyawar dangantaka da fahimtar juna da abokan huldar mu da ke kowane sashe  wanda hakan ya sanya harkokinmu suke kara samun nasara kwarai da gaske.
Aminiya: Ya ya batun tsaro kan manyan hanyoyi domin a wasu lokutan kuna korafin rashin tsaro kan hanyoyi?
Shakka babu yanzu an samu cikakken tsaro a kan hanyoyin mu domin muna kai dabbobi ko’ina ba tare da muna gamuwa da wata matsala ba, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi abin yaba wa ta fuskar tsaro a kasa baki daya. Sabanin yadda al’amura suke a baya, sannan an samu ci gaba ta fuskar fataucin dabbobi da muke yi fiye da lokutan baya.
Aminiya: Ko akwai wasu abubuwa da suke addabar masu fataucin dabbobi tun da ka ce akwai tsaro kan hanyoyin kasar nan?
Babban abin da ke dabaibaye harkar fatauci shi ne yadda ake takura mana wajen karbar haraji kan hanyoyi musamman idan muka haura zuwa kudancin kasar nan. Ana karbar haraji kusan a ko’ina  wanda gaskiya abin ya yi yawa. Muna rokon gwamnatin tarayya dana jihohin da muke shiga da su sassauta mana ta yadda za mu ji karfin gwiwar ci gaba da kai dabbobi cikin nasara.
Yana da kyau mu biya haraji a inda muka loda dabbobi sannan mu biya a inda muke sauke wa wanda shi ne muke fata, amma yadda abu yake yanzu gaskiya muna shan wahala wajen kashe kudade masu tarin yawa dangane da haraji kan hanyoyi.
Wasu lokutan ma mukan rasa mambobinmu ta hanyar harbi da bindiga na jami’an tsaro kan kudi kalilan wanda ko kadan hakan ba daidai ba ne. Sannan ina jaddada cewa masu fataucin dabbobi mutane ne masu bin doka da ka’idojin kowace jiha ta kasar nan, don haka ina fata za mu samu sassauci wajen haraji idan mun dauki dabbobi zuwa sassan kasar nan.
Aminiya: Yanzu ana cikin yanayi na tabarbarewar tattalin arziki, ya ya  cinikin ku yake a  wannan hali da ake ciki?
Babu shakka kowa ya san halin da ake ciki na karancin kudi a kasar nan dama duniya baki daya. Sai dai ina so a fahimci cewa wannan yanayi daga Allah ne kuma shi ne muke ta roko ya  kawo mana karshen abin. naji wasu suna dora alhakin wadannan matsaloli kan  wannan gwamnati ta maigirma shugaban kasa  Muhammadu Buhari, wannan kuskure ne domin shima haka yazo ya tarar da kasa  cikin wannan yanayi kuma  kowa yasan cewa yana kokari kwarai da gaske wajen ganin ana  daukar matakai na rage radadin da al’umma ke ciki.
Yana da kyau mu al’ummar Najeriya mu rika fahimtar yadda lamura suke tafiya mu kuma  tsaya mu ci gaba da addu’a da neman samun saukin al’amura domin na hakikance nan gaba kadan za a samu daidaito na zamantakewa ta kowane fanni na rayuwa. A daina danganta halin da ake ciki da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, abin daga Allah ne kuma zai magance mana in sha’Allah.
Aminiya: A harka irin ta kasuwanci ana yin hulda ba tare da kudi ba wato mutane su karbi kaya sai sun sayar su ba da kudi, ko kuna irin wannan harka?
Idan muka fahimci mutum mai rikon amana ne muna ba shi kaya ya tafi sai ya sayar ya kawo kudi, hakan ce ma ta sanya a kungiyar mu kowa yake cikin rufin sutura da mutunta juna  da kuma yarda da juna walau mutanen mu na arewaci ko wadanda suke mazauna kudanci kuma Alhamdulillah kwalliya tana biyan kudin sabulu.
Aminiya: Ko kana da wani sako ga ’ya’yan kungiyarku da abokan huldar ku?
Sakona ga mambobinkkungiyar mu shi ne a ci gaba da rike amana da tsare gaskiya. A gu ji yin duk wata hulda wadda za ta kawo rashin  jituwa da juna  walau tsakanin masu kaya ko masu saye ko su kansu direbobin da muke aiki da su. Sannan ina fata dukkan abokan huldar mu za su gane cewa fataucin dabbobi abu ne mai bukatar hadin kai da yin hulda  cikin amana da gaskiya, don haka mu shugabanni a shirye muke da mu ci gaba da bullo da sahihan hanyoyi na bunkasa sana’ar mu ta yadda za ta amfani kasa ta kowane fanni.
Hakazalika, ina rokon jami’an tsaro da ke aiki kan hanyoyin mota da su rika yin hakuri da masu fataucin dabbobi tare da ganin ana warware kowace irin matsala cikin ruwan sanyi. Ta yadda komai zai tafi yadda ake bukata.