✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan Fulani ne ya sa ake dora mana kowane laifi – Ardon Toro

Ardon Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi Alhaji Muhammed Inuwa Ahmed ya yi kira ga wadanda suke kusa da shugabanni da sauran al’ummar kasar…

Ardon Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi Alhaji Muhammed Inuwa Ahmed ya yi kira ga wadanda suke kusa da shugabanni da sauran al’ummar kasar nan su rika bai wa shugabanni shawarwari nagari da za su kawo zaman lafiya da ci gaba a kasar nan.

Ardon ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a fadarsa da ke garin Toro. Ya ce bai wa shugabanni shawarwari nagari tare da aiki da shawarwarin shi ne zai magance matsalolin da ake fuskanta a kasar nan.

Har ila yau, ya yi kira ga al’ummar Fulanin kasar nan su mayar da hankali wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Ya ce al’ummar Fulani su yi kokari su kiyaye dukkan abin da zai kawo rashin zaman lafiya a Najeriya, musamman ganin irin abubuwan da suke faruwa a kasar nan na rashin zaman lafiya da ake dora musu.

“Saboda al’ummar Fulani sun fi kowa yawa a kasar nan ne ya sa ake dora musu komai na laifi a kasar nan. Wadansu suna shigar Fulani ne su aikata abubuwan da ba su dace ba, don a rika cewa Fulani ne. Don haka muna kira ga al’ummar Fulani su hada kai, don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya,” inji shi.

Kuma ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta gyara manyan hanyoyin kasar nan, tare da gudanar ayyukan raya kasa.