A tsarin zamantakewar dan Adam ta yau da kullum dole ne a rika samun sabani a rayuwar da ake gudanarwa. Saboda tasirin bambance-bambance na halaye da kuma dabi’u da aka halicci mutum da su. Hakan ke sa ra’ayoyin jama’a ke bambanta da juna, akwai matukar hikima da Ubangiji ya yi amfani da ita akan haka. Hikimar a nan ita ce domin kowa ya amfana da juna, saboda kowane mutum yana tare da wata baiwa da Allah ya halicce shi da ita.
Kowane mutum ya kamata a ce ya fahimci haka, domin mu rika yi wa juna uzuri da kuma warware sabaninmu cikin ruwan sanyi da kuma salama, domin samun kyakkyawar zamantakewa da kaunar junanmu.
Tun bayan da Turawa ‘yan mulkin mallaka suka hade sassan kasar nan da kuma dunkulesu a matsayin kasa guda da ta amsa sunan Najeriya a 1914, akwai al’amura masu yawan gaske da suka biyo baya na dadi da kuma akasin haka. Saboda bambancin da ke tsakanin al’umma tun daga addini da al’adu da yare da tsarin zamantake.
Kusan abu biyu ya kawo zaman lafiya a tsakanin al’umma a waccan zamani, na farko karfi da Turawan mulki mallaka ke da shi, wanda ya yi matukar tasiri wajen shugabantar al’umma. Dole mutum ya yi biyayya ko ya ki ko ya so. Saboda masu jajayen kunnuwa ba sa daukar raini ko wargi.
Shirin da suka shigo da shi kasar nan ba na wasa ba ne, ala tilas kowa ya mika wuya, sun nuna misali a aikace ga wadanda suka yi musu turjiya, ta hanyar murkushesu da karfin tsiya.
Abu na biyu da ya taka rawa shi ne kyakkyawar tarbiyya da kuma girmama juna tsakanin al’umma mabambanta addinai da al’adu. Duk wanda ya kulla alkawari a waccan zamani zai yi matukar kokarinsa don ganin ya cika shi.
Bayan fadi tashi da kuma nasarar samun ‘yanci kai a 1960, shugabannin da suka fara mulkar kasar nan sun yi matukar kokarinsu akan dora kasar bisa kyakkyawar turba. Da kuma shimfida mulki mai cike da adalci da kyawawan misalai a aikace.
Tafiya ba ta yi nisa ba suka fara samun sakon barazana ga rayuwarsu daga wasu makiya, wadanda suka kasance asalin wadanda suka jefa kasar nan cikin dukkan halin da ake ciki shekaru masu yawa.
Sun aikata mummuna manufarsu akan wannan jaririyar kasar da ke cikin tsumman goyo a 1966. Tun daga waccan lokaci kasar nan ta fada cikin rikicin kabilanci da na addini, har zuwa yau an kasa warwareshi domin samun dauwamanmen zaman lafiya.
A dukkan tsarin mulkin da aka tafiyar da kasar nan tun daga soja zuwa farar hula da ke gudanawa a wannan zamani. Babu daya da ya samu nasarar yakar miyagun dabi’u da aka shuka a zukatan al’umma na tsanar juna, saboda kawai muna da bambanci addini da kuma yare.
Idan muka yi duba da tsararrakin kasar nan a duniya, wadanda tuni sun yi mana nisa mai tazarar gaske ta fuskar ci gaban zamani na kimiyya da fasaha. Muna nan kullum a kan matsalar ilimi da ruwan sha da hasken lantarki da kiwon lafiya da kuma noma. Ga shi muna tunkarar shekaru 60
muna da mulki a hannunmu cikin kasarmu ta gado.
Abin tambaya yaushe Najeriya za ta zauna lafiya? Ko a haka za mu yi ta tafiya har bayyanar Mahadi? kasa dai tamu ce, mu ke rayuwa cikinta saboda haka lokaci ya yi da za mu fada wa juna gaskiya, mu rungumi kasarmu da zuciya daya, don kaiwa ga nasara. Allah Ya taimakemu.
Injiniya Jibril Abdul Daura. 08038997861, 08022997340