✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a fara Gasar La-Liga ta Sifen

A yau Juma’a 18 ga watan Agusta ne, za a fara Gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga.  Idan za a tuna…

A yau Juma’a 18 ga watan Agusta ne, za a fara Gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga.  Idan za a tuna a makon jiya ne aka fara gasar rukunin firimiya a Ingila amma a Sifen sai a yau ne gasar za ta fara.

kungiyar kwallon kafa ta Leganes za ta hadu ne da kungiyar Deportibo Albes a yau Juma’a da misalin karfe bakwai da kwata na dare agogon Najeriya.  Wasa na biyu kuma zai gudana ne a tsakanin kulob din balencia da Las Palmsa da misalin karfe 9 da kwata na dare aggon Najeriya.

Sai a gobe Asabar kuma wasannin da za a yi sun hada ne da na Celga bigo da Real Sociedad da misalin karfe biyar da kwata na yamma agogon Najeriya sai Girona da Atletico Madrid da karfe bakwai da kwata na dare agogon Najeriya sai wasan Sebilla da Espanyol da misalin karfe tara da kwata na dare agogon Najeriya.

A jibi Lahadi kuwa kulob din Atletic Club ne zai kece raini da na Getafe da misalin karfe biyar da kwata na yamma sai Barcelona ta hadu da Real Betis da misalin karfe bakwai da kwata na dare sai wasan Deportibo La Coruna da na Real Madrid da karfe tara da kwata na dare agogon Najeriya.

A ranar Litinin ne za a gudanar da sauran wasannin inda kulob din Lebante zai hadu da na billareal da misalin karfe bakwai da kwata na dare sai wasan Malaga da Eibar da misalin karfe 9 na dare agogon Najeriya.

A kakar wasan da ta wuce, kulob din Real Madrid ne ya zama zakara a wannan gasa, don haka zai iya kokarin ganin ya ci gaba da rike kambunsa yayin da sauran kulob da za su fafata a gasar za su yi kokarin kwace wa daga hannun Madrid din.