✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yau take Sallah a Najeriya da Saudiyya

Miliyoyin Musulmai na bikin Sallah bayan kammala azumi 30.

A ranar Alhamis gama-garin al’ummomin Musulmin Najeriya da Saudiyya da wasu kasashe ke bikin Sallah Karama, bayan cika azumi 30 a watan Ramadan shekarar 1442 Hijiriyya.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya sanar ta bakin Kwamitin Ganin Wata na Kasa a ranar Talata da dare cewa ran Alhamis za a yi Sallar.

A safiyar Musulmi za su yi dandazo domin halartar masallatan idi a sassan duniya cikin ado da farin ciki tare da taya juna murnar kammaluwar watan Mai Alfarma.

Musulmi sun shafe kwana 30 na watan Ramadan din bana, kamar bara suna gabatar da ayyukan ibada domin neman kusanci ga Mahaliccinsu.

A sakonsa na taya Musulmi murnar Karamar Sallar, Shugaba Buhari ya bukaci “Mu hada kai wurin yin addu’o’in ganin bayan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da masu neman cimman manufar siyarsarsu ta hanyar ganin Najeriya ta wargaje.

“Mu guji son zuciya, ina kuma rokon shugabannin addini, da na siyasa da sarakuna da su ba wa al’ummominsu kwarin gwiwar rungumar juna da zaman lafiya.”

Tuni dai manyan shugabanni daga bangarori daban-daban na Kasar ke taya Musulmi murnar Sallah, tare da kira da a ci gaba da dabbaka darussan da suka koya a watan Ramadan.

Sallar gama-garin ta nana na zuwa ne bayan a ranar Laraba shehin malamin Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi ya jagoranci mabiyansa sun yi sallar idi, bisa hujjar da cewa sun ga wata.

Kazalika wasu mabiya kungiyar Izala a Jihar Zamfara, sun gudanar da sallar idin a ranar ta Laraba, bisa irin wannan dalili.

A makwabciyar Najeriya, wato Jamhuriyar Nijar ma, a ranar ta Labara aka gudanar da Sallah Karama, bayan hukumomin kasar sun sanar da ganin wata.