A yau ake bikinin Ranar Hausa ta Duniya wadda a duk shekara ake gudanarwa a ranar 26 ga watan Agusta.
Taken ranar a wannan shekara shi ne Raya Sunaye na Hausa.
- ‘A daki daya muke kwana da Tsohon Sarkin Kano Sanusi’
- Wasu daga cikin manyan sarautu da Masarautar Zazzau ta aro daga Borno
Daya daga cikin manyan manufofin Ranar Hausa ta Duniya shi ne ganin harshen Hausa ya samu wurin zama a manyan cibiyoyin duniya irinsu Majalisar Dinkin Duniya a matsayin harshen da ke wakiltar nahiyar Afirka.
A ranar 26 ga watan Agusta, 2015 ne aka fara a bikin Ranar Hausa a shafin sadarwa na Twitter.
Abdulbaki Jari ne ya assasa Ranar Hausa a matsayin wata hanya wadda za a zaburar da matasa domin su rungumi harshensu da al’adunsu masu kyau.
Daga bisani sai bikin ya watsu a sauran kafafen zumunta da gidajen yada labarai.
A shekarar 2020 da ta wuce, an yi bikin a sama da kasashe 15 a fadin duniya cikinsu har da Faransa da Amurka da China da kuma a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Hausa dai shi ne harshe mafi girma a Afirka, kuma mutum sama da miliyan 150 ne ke anfani da harshen a fadin duniya.
Akwai manyan jami’o’i a fadin duniya wadanda suke koyar da Hausa, da kuma manyan kafafen yada labarai na duniya da ke amfani da harshen.