✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau mata za su fara kallon kwallon kafa a Saudiyya

Rahotannin da ke fitowa sun nuna a yau Juma’a 12 ga watan Janairun 2018 ne kasar Saudiyya za ta amince wa mata su rika shiga…

Rahotannin da ke fitowa sun nuna a yau Juma’a 12 ga watan Janairun 2018 ne kasar Saudiyya za ta amince wa mata su rika shiga filayen wasanni don kallon kwallon wasan kwallon kafa a filayen wasanni daban-daban da ke fadin kasar.

Wannan shi ne karo na farko da Saudiyya ta amincewa mata su shiga filin kwallo a tarihin kasar.  Wasan farko da matan za su kalla a yau shi ne wanda zai gudanaa tsakanin kulob din Al-Ahli da kuma na Al-Batin wanda za a yi a babban filin wasa na Riyad.  Sai kuma wanda za a yi a Gabashin kasar a filin wasa na Damma kamar yadda wata sanarwa da Ma’aikatar watsa labarai ta kasar ta fitar a ranar Litinin da ta wuce.

A watan Satumbar bara ne Sarkin Saudiyya ya sanarwa duniya cewa daga watan Janairun 2018 ne za a fara ba mata dama su rika shiga filayen kwallo suna ganin yadda wasannin za su gudana kai-tsaye da hakan ya janyo ce-ce-ku-ce daga wadansu kasashen Musulmi a fadin duniya.