A yau Litinin ne kotun kolin za ta yanke hukunci bayan daukaka kararrakin zabukan Gwamnonin da suka hada da: Gwamnan jihar Kano Umar Ganduje, Gwamnan jihar Sakkwato Waziri Tambuwal da kuma Gwamnan Imo Emeka Ihedioha.
Majiyarmu ta samu rahoton cewa, idan akwai yiwuwar daukaka karar za a yi hakan ne bayan saurarar kararrakin zabukan Gwamnonin.
A wani bangaren kuma akwai kararrakin da aka daukaka karar su, na Gwamnoni bakwai da suka hada da: Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri; Gwamnan Bauchi Bala Mohammed; Gwamnan Benuwe Samuel Ortom; da Gwamnan jihar Filato Simon Lalong.